Kungiyar malaman jami’o’i a Nigeria ta bayyana cewa ta tsawaita yajin aikin da take yi da makwanni 8 ne, sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta gaza gamsar da su kan alkawarin dake tsakaninsu.
Shugaban kungiyar na kasa Emmanuel Osodeke, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Litinin.
Emmanuel Osodeke ya kuma ce a yayin taron majalisar koli ta kungiyar wanda ya gudana ranar Lahadi, ya ce sun amince da sake baiwa gwamnatin tarayya waadin watanni biyu, domin ta cika musu alkawura dake tsakaninsu, wanda kuma hakan ne zai baiwa daliban jami’o’in damar komawa ci gaba da karatunsu.
Yanzu dai dalibai na ci gaba da nuna damuwarsu kan yadda karatunsu yake samun koma baya, suna masu cewa wannan matsalar kusan akan su tafi tasiri sama da kowa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wannan yajin aikin na zuwa a kasa da shekara guda da kungiyar ta kamala wani mai tsawo wanda shima ya shafe watanni {9} kungiyar na gudanar da shi.