By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin tarayya tace tana ci gaba da duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna data rattabawa hannu da kungiyar malaman jami’o’i.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Abuja.
A ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021 ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni uku kan gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatun ta.
Malaman sun kuma yi barazanar sake yin wani zagayen yajin aikin na harkar masana’antu, biyo bayan rashin amincewar da aka yi wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattaba hannu da kungiyar wadda aka dakatar da yajin aikin na shekarar 2020.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar 5 ga watan Disamba, 2021 ya koka da cewa duk da ganawar da ministan kwadago ya yi, yace daya kawai daga cikin bukatun da ASUU ta nema aka biya.
Da wakilinmu ya tuntubi Ngige kawai yace ana ci gaba da bitar yarjejeniyar MOU.
Sannan yace, “Ana ci gaba da tsare-tsare na duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyar MOU. Za mu sake duba wadanda aka gana da wadanda ba a gamu dasu ba”.
A halin da ake ciki kuma, a ranar Juma’a majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa ASUU za ta yanke shawara kan ko za ta tafi yajin aikin ko kuma a’a, biyo bayan sakamakon tarurrukan da aka shirya yi na shiyya-shiyya da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Disamba, 2021.
Hakazalika majiyoyin da suka zanta da wakilinmu sun raba wata takarda da ke kunshe da baje kolin wuraren da za a gudanar da tarukan shiyyar.
Wakilinmu ya bayyana cewa za a gudanar da tarukan ne tsakanin 9 ga watan Disamba zuwa 15 ga watan Disamba a Abuja, Nsukka, Ibadan, Yola, Benin, Akure, Lagos, Bauchi, Owerri, Fatakwal, Calabar, Sokoto da kuma Kano.
“Shawarar tafiya yajin aikin ko a’a zai dogara ne akan sakamakon tarurrukan da za a yi daga kowace shiyya”. Majiyar ta kara da cewa.