Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, ya karbi riga-kafin cutar COVID-19 (Pfizer). Ana sa ran cewa shi ne dan Nigeria na farko da aka fara yi wa allurar riga-kafin cutar.
Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku, ya tabbatar da wannan ci gaban ga jaridar TheCable a ranar Alhamis.
An yi wa Atiku Abubakar allurar riga-kafin COVID-19 ne a Dubai, da ke a daular Larabawa.
“Muhimmancin yin allurar riga-kafin COVID-19 domin dakile yaduwar cutar korona ba zai iya misaltuwa ba, musamman ma a kasashen Africa da Nigeria.
KARANTA WANNAN: Donald Trump ya amince zai mika mulki a ranar 20 ga watan Janairu
“A jiya (Laraba), a loton da ake gudanar da riga-kafin cutar a fadin duniya, mai girma Atiku Abubakar ya karfi allurar Pfizer-BioNTech wacce ake yi domin riga-kafin COVID-19,” a cewar hadimin Atiku.
“Yana kuma sa ran ‘yan Nigeria, musamman masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da wadanda ke fama da rashin lafiya, za su karbi wannan riga-kafin a cikin kasar.
Allurar Pfizer itace allurar farko da hukumar lafiya ta duniya WHO, ta amince a yi amfani da ita a matsayin riga-kafin COVID-19 na gaggawa, kuma a cewar Pfizer da BioNTech, allurar na yin magani da kashi 90.
Haka zalika, gwamnatocin kasashen UK, US, Malaysia da Switzerland sun amince da yi wa ‘yan kasarsu wannan allurar riga-kafin, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Gwamnatin Nigeria ta ce tana jiran isowar akalla allurori miliyan 20 na COVID-19 a farkon shekarar 2021, kuma shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad ya ce babu wani dan Nigeria da zai tsira daga wannan riga-kafi.
Real wadda take ta biyu a teburin L Liga ta shiga shekarar 2021 da kafar dama, bayan da ta doke Celta Vigo 2-0 a gasar Spaniya ranar 2 ga watan Janairu a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
A watan na Janairu za ta fafata a karawa uku a La Liga, da daya a Spanish Super Cup wanda ta lashe a bara a Saudiyya da kuma fafatawa a Copa del Rey.
Ranar Asabar, Real za ta ziyarci Osasuna domin buga gasar La Liga karawar mako na 18.