Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin Shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar PDP, yace babbar Sallah wata hanya ce da zamu tuna yadda zamu kawo sauyi a matsalolin Najeriya. Jaridar Pmnews ta ruwaito
A wani jawabi daga gareshi yake cewa, wannan wata alfarma ce da Allah da ya sake bamu damar ganin wannan lokacin, mu kuma godema Allah da ya bamu hakan, zamuyi bikin Sallah tare da iyalan mu.
Yace babbar Sallah na tuna mana Ibadu kamar su layya, soyayya tare da sada zumunci.
KARANTA:- Zan iya sadaukar da rayuwata don tabbatar da tsaro a jaha ta, Gwamna Bungudu
A matsayin ka na musumi a babbar Sallah ya kamata muyi koyi da tarihin Annabi Ibrahim A.S tare da Dan sa Ismail A.S, Yana nuna mana cewar mu zama al’umma daya.
A wajan gudanar da bikin Sallah dole mu kasance masu hakuri da juriya da kuma yafiya, Wanda wannan shine hanyar da ya kamata mubi don cigaban kasarmu da maganin abunda ke damunmu.
Kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya koyar, yin layya a wannan lokacin na kara albarka da soyayya ga ayyukan mu da kuma addu’oin mu.
Sannan babu yadda za’a yi musamu soyayyar Ubangiji matukar za’a cigaba da kisan bayin Allah, ana cigaba da yada karai rayi a tsakaninmu, wanda kuma hakan ya ruga ya zama dabi’un mu.
Atiku Abubakar ya taya daukacin al’ummar Musulmai murnar babbar Sallah, sannan yana musu tuni kan cewar babu wani da yafi wani sai wanda yafi Jin tsoran Allah.
A wani labarin Kungiyar Musulmai ta JNI tana yima daukakin al’ummar Musulmai murnar babbar Sallah
Babbar kungiyar Musulunci ta Jama’atu Nasrul Islam (JNI) tana yima daukakin al’ummar Musulmai murnar babbar Sallah.
Sakataren kungiyar Khalid Aliyu, ya sanar da haka a Kaduna.
Kamar yadda yawabin ya fito, Karkashin jagorancin Kungiyar ta JNI Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id, na taya daukacin al’ummar Musulmai murnar babbar Sallah”
“Muna rokon Allah ya sanya sunayenmu cikin wadanda zai karbi ibadunsu da layyansu cikin wadadannan kwanaki.”
“Allah baya bukatar jinenan abunda muka yanka ko naman su.” Kamar yadda Aliyu yace
Sakataren kungiyar ya tunatarma al’ummar Musulmai da suyi azumi a yau Litinin na yinin ranar Arafa.
Kada mu manta da ambaton Allah a koda yaushe, mu gode masa bisa ni’imarsa.
Ya kuma kira sauran Yan uwa Musulmai da suyi taka tsan-tsan da hali na tsaro, gami da bin dokar Covid-19.
Yace za ayi amfani da Jami’an tsaro wajan tabbatar da kawo zaman lafiya a wannan kasar.
Mun kuma bukaci gwamnati data kara himma wajan daukan matakai na tsaro.