A yayin da shirye-shiryen zaben 2023 ke kara karatowa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon ubangidansa, Cif Olusegun Obasanjo da Alake da kuma babban mai rike da sarautar Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo.
Atiku, wanda ya isa harabar gidan Olusegun Obasanjo da misalin karfe 10:10 na safe. sun shiga ganawar sirri da Obasanjo, inda suka kwashe kusan awa daya.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri, Atiku ya ce, ‘Na zo ganin maigidana’ amma ya yi shiru kan abin da aka tattauna a taron.
Ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su kara jajircewa wajen yin takara da dattijai a zaben 2023, ciki har da ofishin shugaban kasa, inda ya ce neman a tauye tsofaffin hakkinsu na tsarin mulki na neman cimma burinsu na siyasa ba daidai ba ne.
Ya yi nuni da cewa filin zaben yana bude ga matasa ‘yan takara, amma ya nuna kwarin guiwar cewa har yanzu zai samu tikitin jam’iyyar na tsayawa takara a wannan mukami a shekarar 2023.