Babu shakka mai martaba Lamidon Adamawa, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa adalin jagora ne ga al’umarshi kuma abin koyi ne ga sauran shugabanni na kasar nan.
A wannan lokaci da yake cika shekaru 10 a kan karagar mulki, ina da yakinin cewa Lamido basarake ne wanda ya yi fice kuma yana tafiyar da mulki tare da ilmi.
Maimartaba Lamido yana samun jinjina daga jama’a saboda hangen nesa wajen shimfida adalci da hada kai ga jama’ar masarautarshi.
A matsayina na Wazirin Adamawa, bani da kokwanto a kan cancanta da kwarewar Muhammadu Barkindo. Ya zuwa yanzu ya tabbatar wa kowa cewa ya gaji halayen mahaifinshi wato Marigayi Lamido Aliyu Musdafa.
Tun lokacin da aka nadashi a matsayin Lamidon Adamawa shekaru goma da suka wuce nake lura da tsarin mulki irin nashi. Ina so in jaddada cewa na gamsu kwarai da yadda yake gudanar da harkokin mulki tare da cancanta, harma a ce a jaha mai yawan kabilu irin Adamawa.
Na shaida cewa Lamido na gudanar da mulki tare da la’akkari da zamani da tsinkayen kyautata rayuwar jama’a. Na yi amanna cewa, irin wannan salon mulkin, wanda abin koyi ne, yana da tasiri matuka.
Ina alfahari da kasancewa basarake a fadarshi saboda na yarda da hangen nesa irin nashi wanda burinshi shine, ci gaban al’ummarmu na jahar Adamawa da kasa baki daya.
Ina mika sakon taya murnata ga Lamido Adamawa a wannan lokaci na murnar shekaru goma a kan gadon sarauta.
Ina rokon Allah Ya kara mashi lafiya da tsawon kwana domin al’umarmu su ci gaba da samun kyakkyawar rayuwa mai dorewa.
Alhaji Atiku Abubakar
(Wazirin Adamawa).