Babbar Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Atiku Abubakar Mai Suna Louis Okoroma ya riga mu gidan gaskiya.
Mr. Okoroma ya mutu ne a ranar Alhamis din da ta gabata wata biyu bayan rasuwar Mai dakin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar.
Cikin wata sanarwa da Babban Shugaban Ofishin Yada labaran Atiku Paul Ibe yace ko da a ranar laraba kwana guda kenan gabannin mutuwar Okoroma suna tare a gurin aiki, to Ashe ganin karshe kenan da za suyi da juna.
Mr. Ya bayyana Mamacin a matsayin jajirtacce Kuma haziki Wanda ya sadaukar da lokacin shi wajen aiki, musamman ma aikin shi na jarida.
Daga bisani ya bayyana yadda Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana alhinin shi bisa wannan babban rashi tare da mika ta’aziyar shi ga yan uwa da iyalan mamcin.