A yau Asabar Toshon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar a jihar Adamawa, ya tarbi dubbun dubatar mutane da suka sauya sheka daga wasu jam’iyun siyasa, zuwa Jam’iyar Adawa ta PDP.
Atiku tare da Gwamnan jihar Ahmadu Fintiri, sun tarbi masu sauya shekar ne a filin wasa na Ahmadu Ribadu Square, dake Jimeta a Yola babban birnin jihar.
Sai dai mafi yawaicin jagororin yan siyasan a cikin mutanen, sun fito ne daga jam’iya Mai Mulki ta APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yaro Dan shekara 5 ya afka Rijiya a. Kano
Daga cikin jagororin sun hada da Mr Kobis Aruthemnu Tsohon sakataran gwamnatin jihar Adamawa, da kuma Mallam Bello Jada sanan nan dan Siyasa da ake kira da Calculate.
Sauran sun hada da Honorabul Nedo Kufaltu, Commodore Saki Bodes Mai ritaya, Mr Philips Gatua da kuma Daniel Bwala wadanda suka fito daga Yankin Tsakiyar jihar da kuma Kudancin Jihar.
Atiku, da ya yi magana cikin harshen Hausa a wurin taron, ya ce, ” An yafe muku kura -kuran ku na kasance wa cikin jam’iyar APC a baya, kuma Ina Mai sanar da ku cewa PDP na shirin karbar mulki a shekarar 2023″ inji shi.
Ana shi jawabin gwamnan Fintiri ya yi wa sabbin mammobin Jam’iyar PDPn alkawarin basu dama a cikin gwamnatin sa, domin dama wa da su.
Shi kuwa Shugaban jam’iyar PDP na Jihar Adamawa Tahir Shehu ya ce, shigowar sabbin mambobin cikin jam’iyar PDP na nuna durkushewar sauran jam’iyun siyasa.
A karshe Kanar Andrawus Sawa mai Ritaya, Wanda ya yi jawabi a madadin sauran sabbin mambobin, ya ce, kyawawan manufofin jam’iyar PDP ne suka sanya su sauya sheka zuwa cikin jam’iyar.
Comments 1