A ranar Asabar ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai ziyarar jaje a jihar Katsina.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 ya ziyarci iyalan Dahiru Mangal, wani hamshakin dan kasuwa a jihar ta Katsina.
Hajiya Murja Bara’u, mahaifiyar attajirin mai shekaru 85, ta rasu ne a ranar Alhamis, kuma an yi jana’izarta a ranar Juma’a.
Atiku ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya saka mata da Aljannar Firdausi.
Ya wallafa hotunan ganawar da yayi da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Gwamnan Yobe, Mai Buni; da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari.
Wanann dai shine karo na biyu da aka yi wa Mangal rasuwa cikin kasa da shekara guda. Ɗansa, Nura, ya mutu a watan Maris 2021 a wani hatsarin babur.
Wanda ake yi wa kallon babban attajirin Katsina, Mangal shi ne Shugaban Kamfanin Afdin Group, masu kamfanin Max Air, Afdin Petroleum, Afdin Construction, da dai sauransu.
Comments 1