By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim a ranar Juma’a, sun taya tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo murnar cikar sa shekaru 85 a duniya ranar Asabar.
Atiku ya bayyana tsohon ubangidan nasa a matsayin wakilcin kyakkyawan shugabanci da kuma kishin kasa baki daya.
Atiku, wanda ya yi aiki a karkashin shugabancin Obasanjo, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu domin bikin cikar Obasanjo shekaru 85 da haihuwa mai taken, ‘Obasanjo ya kafa tsarin mika mulki a dimokuradiyya, kawo sauyi a Najeriya, Afrika – Atiku’.
A cewarsa, “Bikin na Obasanjo ya yi daidai da murnar hangen kyakkyawan shugabanci da kuma kishin kasa baki daya.
“Hanyoyin da Obasanjo ya kawo kan mulki ko dai a matsayin shugaban gwamnati na soja ko kuma a matsayin zababben shugaban kasa ta hanyar dimokuradiyya na ci gaba da kafa hanyar samar da kyawawan manufofin ci gaba a gwamnatocin Afirka.
“A cikin shekaru 70 da suka wuce na karshen lokacin da kusan daukacin Afirka suka mamaye mulkin kama-karya na soja, Obasanjo ya kafa hanyar mika mulki ga gwamnatin farar hula a Najeriya, kuma wannan kokari daya tilo ya fara aiwatar da tsarin dimokradiyya a fadin nahiyar.
“Obasanjo ya kirkiro wani zamani na kawo sauyi a Najeriya wanda ke ci gaba da amfanar al’ummar Najeriya har zuwa yau, kuma shi ya sa yake ci gaba da jin dadin ‘yan siyasa da jahohi masu son ci gaba ba kawai a Afirka ba har ma da duniya baki daya,” inji shi.
A nasa jawabin, Sanwo-Olu, ya ce tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya rubuta sunansa da zinare.
A cewar gwamnan jihar Legas, Obasanjo ya cancanci a yi murna da shi, kasancewar ya yi wa Najeriya hidima a bangarori da dama, musamman don hadin kai, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da ci gaban Nijeriya, sannan kuma ya zama shugaba mai matukar muhimmanci a duniya.
Sanwo-Olu, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa Mr.Gboyega Akosile, a ranar Juma’a ya ce Obasanjo ya kasance daya daga cikin ’yan Najeriya kadan daga cikin shugabannin Najeriya da suka bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban kasar a matsayinsa na shugaban soja da na farar hula kuma ya bar baya da kura.
Kazalika Sanwo-Olu ya ce, “A madadin iyalaina da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Legas, ina taya Cif Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 85 da haihuwa.
“Baba Obasanjo ya cancanci a yi murna da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarmu, musamman hidimar da ya yi wa kasa a matsayinsa na babban hafsan soja, shugaban kasa kuma shugaban Tarayyar Najeriya.”
Hakazalika, Sanata Anyim Pius Anyim ya kuma bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin fitaccen shugaba wanda ya nuna himma wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya da Afirka.
Dan takarar shugaban kasa a cikin sakon taya murna da ya sanyawa hannu ya bayyana cewa Obasanjo ya taka rawa a matakai daban-daban na tarihin siyasar Najeriya da Afrika.