Tsohon mataimakin shugaban ƙasar nan kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nemi majalisar dattawan nan da ta dakatar da bai wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari duk wata dama ta karɓo bashi a nan gaba.
Atiku ya aike da wasiƙar ga shugaban majalisarbSanata Ahmed Lawan, inda ya buƙaci a jingine bai wa Shugaban ƙasar damar sake karɓo bashin da a cewarsa ba ya tsinana wa ƙasar komai.
https://dimokuradiyya.com.ng/majalisa-ta-amince-wa-shugaba-buhari-ciwo-bashin-dala-biliyan-5-5/
Atiku ya ce Najeriya za ta iya shiga tsaka mai wuya muddin aka ci gaba da karɓo bashi duba da wadanda aka karɓa a baya ba su haifar wa ƙasar wani da mai ido ba.
A ƙididdigar da Ofishin kula da basussuka na ƙasa (DMO) ya fitar a watanni biyu da suka gabata, ya nuna cewa a rubu’in farko na bana, bashin da ya yi wa ƙasar kanta ya kai Dala miliyan 79.3.