Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasuwar Kantin-Kwari da ke Kano. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayar da gudunmawar ne a ranar Litinin, a Kano, a wani taron karbar tsohon gwamnan jihar Kano, Sen. Ibrahim Shakarau, a cikin jam’iyyar daga New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa daruruwan shaguna ne bala’in ya shafa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dokokin Kano Zata binciki Musabbabin Wata Ambaliyar Ruwa A Jihar
“Muna so mu yi amfani da wannan damar wajen jajanta wa ‘yan kasuwar Kantin-Kwari.
“Mun ji cewa ambaliyar ruwa ta lalata dukiya a Kantin-Kwari a yau.
“Za mu aiko da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda abin ya shafa,” in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Ku Taimaka Mana Wajen Ganin Mun Kama Mr 442 Da Safara’u – Afakallah
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana neman mawakin da ake kira da 442 ruwa a jallo, saboda yin wakokin da basu dace ba.
Shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano, Isma’il Afakallah, ya bayyana cewa wakokin sun sabawa da dokar hukumar.