Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Litinin din nan, ya yi tsokaci kan shirye-shiryen yakin neman zabensa gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Atiku, a wajen taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) karo na 62 da aka gudanar a Eko Hotels, da ke Victoria Island, a jihar Legas, ya ce shirin yakin neman zabensa za a kira shi Unity-SEED.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin din nan.
Karanta kuma: ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Hallara A Wani Taron NBA
Da yake magana a takaice, ya ce Unity-SEED na wakilta “Hadin kai, Tsaro, Tattalin Arziki, Ilimi da Rarraba madafun iko ga jihohi da kananan hukumomi” wanda zai zama tushen tsarin manufofinsa idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya mai zuwa a shekara mai zuwa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Atiku ya bayyana cewa shirin zai yiwu a sake haifuwar Najeriya da al’ummar kasar ke ta kokawa a kai.
Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Na yi amfani da damar taron farko na taron NBA karo na 62, wajen baiwa lauyoyin Najeriya damar fahimtar tsare-tsarena masu jajircewa, wadanda suka hada da hadin kai, tsaro, tattalin arziki, ilimi da mika mulki ga jihohi da kananan hukumomi, wanda aka sani da shi a takaice na Unity-SEED.
“Na jaddada yadda haɗin gwiwar waɗannan ka’idoji guda biyar ke da alaƙa. Na ba su tabbacin cewa sabuwar Najeriya na burinmu mai yiwuwa ne a hannun wani kwararren mutum mai jajirtacewa.”
A wani labarin: PDP Na Tafiyar Hawainiya A Kokarin Sasanta Atiku Da Wike, Tsohon Shugaba
A ranar Jumu’a, wakilan Atiku karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa suka gana da tawagar gwamna Wike a Patakwal, babban birnin Ribas, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dimokuraɗiyya ta fahinci cewa ɓangarorin biyu sun zauna da juna ne da nufin lalubo hanyar sasanta jiga-jigan guda biyu.