Daga: Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa Kano tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Atiku zai karbi bakuncin Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa da ake sa ran za su sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, ranar Litinin mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magoya Bayan Peter Obi Sun Gudanar Da Babban Gangami A Onitsha, Tare Da Rufe Manyan
Cikin wadanda suka sauka a filin jirgin akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali.
A wani labarin kum ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Kaftin Din Soji Na Bogi Mai Yiwa Mata Fashi
Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas sun kama wani Andy Edwards da ya bayyana kansa a matsayin Kyaftin na Sojojin Najeriya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.