Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya jinjina wa wasu mata likitoci ‘yan gida daya.
Daya daga cikinsu ne ta wallafa hotonsu su biyar inda ta ce mahaifinsu guda kuma dukkansu likitoci ne da suka kware a fannoni daban-daban.
Da yake tsokaci a kan hoton, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya ce babu abin da ya fi dacewa ga al’umma fiye da bai wa mace ilimi.
“Abin sha’awa ne. Idan ka bai wa mace ilimi, ka ilimantar da iyali da ma al’umma ne,” in ji Atiku.