Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyar ta soke taron yakin neman zaben ta a jihar Ribas.
A cewar jam’iyyar ta soke Gangamin na ta ne, domin gudun zubar da jini. Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Zanga-zanga Ta Barke A Ogun Kan Karancin Sabbin Takardun Naira
Kakakin kwamitin Charles Aniagwu, a ranar Talata a Asaba, ya kuma ce soke matakin ya zama dole saboda karuwar rashin tsaro a jihar.
Babbar jam’iyyar adawar ta kara da cewa gwamna Nyesom Wike bai kasance barazana gare su ba, musamman kalaman da yake wadanda suke kallon su a matsayin jeka nayi ka.
Aniagwu ya ce jam’iyyar ta fice daga gudanar da taron ne saboda Atiku da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa na ganin burinsu bai kai jinin wani dan Najeriya daraja ba.
Kwamishinan yada labarai na Delta ya bayyana cewa Atiku ya binciki lamarin da ya faru a Rivers kuma ya soke taron, domin gujewa me kaje ya zo.
A wani labarin kuma: FG Ta Amince Da Ɗaga Likkafar Wata Kwaleji A Kano Zuwa Jami’a
Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a ranar Talata ta amince tare da daukaka Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi.
Sakataren zartarwa na hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, a lokacin da yake mika lasisin aiki ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a Abuja, ya ce jami’ar an amince da ita a matsayin jami’a ta 61 a fadin kasar nan.