Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah.
A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin shugaban kasar ya jajantawa iyalan wadanda suka jikkata da kuma wadanda aka kashe a harin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargabar An Kashe ‘Yan sanda, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kaiwa Ifeanyi Ubah Hari
“Ina tausayawa mai girma Sanata.”inji Atiku
“Allah ya sa rayukan wadanda suka rasu su huta lafiya.”
“Muna da ayyukan da za mu yi don tabbatar da cewa tsaro ya dawo kasarmu,” a cewar Atiku.
Rahotanni sun bayyana cewa an kaiwa ayarin motocin dan majalisar hari ne a garin Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da harin kan ayarin motocin Ubah, amma ba ta bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda suka mutu ba.
A wani labarin kuma, Ana Fargabar Mutane 13 Sun Mutu A Karin Wani Hatsarin Kwale-kwale A Jigawa
Mutane 13 ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne da yammacin ranar Lahadi lokacin da fasinjojin suka shiga cikin wani kwale-kwale daga kauyen Dabi zuwa Sayango domin jajantawa iyalansu kan rasuwar wani dan uwansu.