Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta zancen da ake yadawa cewar zai mayar da jami’o’in kasar nan hannun gwamnonin jihoji.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Paul Ibe ya fitar da yammacin ranar Litinin, tare da rabawa manema labarai.
Paul ya ce sun lura an juya maganar da dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya a Legas.
KARANTA ANAN: Najeriya Na Bukatar Shugabanni Da Zasu Tabbatar da Ita a Ƙasa Ɗaya – Okowa
Yayi dogon jawabi ne kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.
Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami’in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.
“Wannan ba daidai ba ne don bai fadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa” in ji shi.
Ya ce abin da Atiku Abubakar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami’o’in da ke karkashinta.
A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi ragamar tafiyar da jami’oi ba gaskiya ba ne, a cewar Paul.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya ta roki Likitoci, Ma’aikatan Jinya da su zauna Najeriya
Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirinta na daukar matakan shawo kan matsalar tabarbarewar kwakwalwa a Najeriya.
Karamin Ministan Lafiya, Joseph Ekumankama ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Ebute Meta, Legas.