Atiku yazo ne domin haɗa kan Najeriya – Iyorchia Ayu
A yayin da ake cikin rikicin jam’iyyar PDP karkashin Jagorancin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu a ranar Alhamis ya bayyana cewa jam’iyyar ta hade.
Ayu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a matsayin wanda zai hada kai Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar NNPP Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Babbar Kotun Tarayya A Kaduna
Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben Shugaban Ƙasa da na gwamna na jam’iyyar a jihar Kwara.
Ayu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tsohuwar jam’iyya mai mulki za ta ceto kasar a shekarar 2023.
A cewar Ayu: “PDP babbar iyali ce guda daya, kuma muna kan hanyar mu ta samun nasara. PDP ta dawo don ceto kasar nan kuma mu jam’iyya ce ga kowa.
“Mun yi babban kuskure ta hanyar sauraron alkawuran da za mu canza, shin kun gamsu da wannan canjin?”
PDP ta fada cikin rikici tun lokacin da ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa.
Wata kungiya da aka fi sani da Integrity group wacce aka fi sani da G-5 ta yi ta tada jijiyoyin wuya wajen ganin an samu daidaito a cikin tsarin jam’iyyar.
Kungiyar karkashin jagorancin Wike na jihar Ribas, ta bukaci Ayu da ya yi murabus daga ofishin shugaban jam’iyyar na kasa.
Sun lura da wani yanki na musamman ba zai iya samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar kuma shugaban kasa ba.
A wani labarin kuma: DSS Ta Janye Karar Da Take Yiwa Tsohon Mai Sasantawa Da ‘Yan Ta’adda, Tukur Mamu
Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta sha alwashin tura gwamna Abdullahi Sule zuwa kasar Saudiyya a shekarar 2023 dake tafe.
Mista Francis Orogu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Karu a ranar Alhamis.
Orogu ya yi zargin cewa gwamnan ya nuna cewa ba shi da ikon gudanar da mulkin jihar inda ya yi takama da cewa PDP za ta kore shi zuwa kasar Saudiyya a karshen wa’adinsa na farko.