Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
A yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama, dangane da fim din da Adam A Zango ya ke shirya wa mai dogon Zango wato “Farin Wata Sha Kallo” a sakamakon cire Ummi Rahab da kuma auren ba zata da ita ma jarumar fim din Zahra Diamond ta yi, ana dab da fara ci gaban aikin.
Ga duk masu kallon fim din dai, za su gane wadannan jaruman biyu a kan su labarin ya ke tafiya, domin labarin ya dakko ne daga lokacin da Ummi Rahab ta ke karama, idan ta girma ta ke zama Zahra Diamond, to ana tsaka da fim din aka yi rabu war Dutse hannun riga tsakanin Adam A Zango da Ummi Rahab, kuma ita ma Zahra Diamond, da ta tafi garin su a Jamhoriyar Niger, da shirin za ta je gida ta yi babbar Sallah ta dawo, sai kawai aka ga ta aiko da sakon ta yi aure, don haka ta na bai wa duk wanda ta ke cikin fim din sa hakuri, domin ba za ta samu damar ci gaba ba, saboda ta yi aure, don haka tana yi musu fatan alheri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta kama yan kungiyar asiri 15 a Nasarawa
Abin da mutane su ke fada musamman a cikin Masana’antar fina-finai ta Kannywood shi ne, mecece makomar fim din Farin wata Sha Kallo? Wacce hikimar za a yi wajen sauya jaruman shirin wadanda za su gamsar da masu kallo? Lokaci da yanayi ne kawai zai bayar da amsar hakan.