Iyayen daliban Makaranta Sakandare na Federal College of Forestry MEchanization dake garin Mando na karamar hukumar Igabin jihar Kaduna sun baiwa gwamntin jihar Kaduna da ta tarayya wa’adin Awanni arba’in da takwas da su kubutar musu da yaya da aka yi garkuwa da su.
Cikin hawaye na tausayi wadannan iyaye sun mika koken su gaya wa Majalisar dinkin duniya da Kungiyar Lauyoyi ta kasa da Kungiyar Malaman Jami’a da ma duk wasu masu fada a kasar cewa su matsa kaimi wa gwmanatin ta kubutar musu da yaya.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Alhamis 11/3/2021 ne dai wasu yan fashin daji suka kutsa wannan makaranta inda suka kwashi yara sama da talatin suka yi awun gaba da su.
Kuma a baya-bayan nan wani faifan bidiyo ya karade duniya inda yake nuna yadda yaran rusa kuka suna kira da gwmnatin da ta taiamaka ta biya kudin fansa kimanin naira miliyan dari biyar da yan fashin dajin suka bukata.
To sai abin takaici kamar yadda iyayen daliban suka bayyana shine yadda hukumomin makarantar da ma gwamnati suka ja bakin su suka yi gum ba tare da nuna irin hubbasar da suke yi wajen ganin an ceto yaran ba.