Awanni bayan lashe zaɓen Fidda Gwani, Kotu ta soke nasarar Ɗan Takarar APC a Abia, Emenike
Babban Kotun Jahar Abia a ranar Alhamis ta yanke hukunci akan wata Shari’a akan nasarar Ɗan Takarar APC na Gwamna Chief Ikechi Emenike, Wanda ya samu nasarar zaben fidda gwani.
Emenike dai a ranar Alhamis aka ayyana shi a matsayin Ɗan Takarar daya lashe zaben Jahar Abia, amma mai Shari’a O. A. Chijoke ya ce nasarar bata inganta ba.
A wata ƙara da Mr. Chinedum Nwole da wasu mutum biyu suka shigar,Mai Shari’ar ya ayyana cewa Emenike bai cancanta yayi Takarar Zaben Fidda Gwani, domin an taɓa korar sa a Jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban SMEDAN Dikko Raɗɗah ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Katsina
Kotu ta yanke hukuncin cewa Emenike da Shugaban APC na Jahar Chief Donatus Nwakpa sun karya dokar Ƙundin Tsarin Jam’iyyar.
Mai Shari’a Chijoke ya ayyana cewa bashi da ikon shiga zabe a matakin mazaɓu, da Ƙaramar Hukuma, da Jaha gami da Babban zaben Jam’iyyar na Ƙasa.
Comments 1