By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin Burkina Faso a ranar Laraba ta bayyana cewa, tana “aiki” don samun ayarin motocin sojojin Faransa da masu zanga-zangar suka hana shiga kasar kusan mako guda inda tace wannan itace “makoma ta karshe”, ta hanyar Mali zuwa Nijar.
Majiyoyin tsaro sun fada a ranar Litinin cewa, ayarin motocin na jira ne a wani shingen sojoji dake tazarar kilomita 30 arewa maso gabashin Ouagadougou.
Muna da makiya a nan, Faransa ba makiyiyiyar mu bace, Bari in fayyace, Faransa kawa ce a yaki da ta’addanci, Faransa na tare da mu a cikin kawancen yakin Sahel, Faransa kasa ce da ke tare da mu a kasa, kuma a duk lokacin da muka nemi Faransa ta shiga tsakani, kamar yadda yarjejeniyar da muka kulla tayin hakan ne idan albarkatunta suka bada izini.”
Ministan ya ba da tabbacin cewa, ayarin motocin da aka nufa zuwa sojojin Faransa a Gao, ba jerin gwanon da ke yakar Burkina Faso ba ne, kuma ba zasu baiwa ‘yan ta’adda makamai ba, kamar yadda wasu bayanan karya a shafukan sada zumunta suka yi ikirarin.
Ministan yace rundunar Jandarma ta kasa ce ke rakiyar ayarin motocin, lamarin daya sa ba za a iya kai wa ‘yan ta’adda makamai ba, in ji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar Asabar, akalla mutane hudu ne suka jikkata a garin Kaya dake yankin arewa ta tsakiyar kasar Burkina Faso, inda masu zanga-zangar ke adawa da wucewar wani babban ayarin motocin sojan Faransa da suka fito daga kasar Ivory Coast.
Tuni dai masu zanga-zangar suka sassauta bayan da ayarin suka shiga Burkina Faso.
Sannan yace, ana gudanar da aikin samar da kayan aiki tare da sojojin Faransa, musamman na jigilar sojojin Burkina Faso zuwa yankunan da ‘yan jihadi ke kaiwa hari.
Faransa wacce ke yankin Sahel tun a shekarar 2013 a yakin da ake yi da kungiyoyin jihadi, ta fara rage yawan mutanen yankin zuwa 2,500 daga maza 3,000 nan da shekara ta 2023 idan aka kwatanta da sama da 5,000 a baya.