A wannan rana ta Talata wato 20 ga watan Oktoba shahararren fim ɗinnan da ya taɓa zuciyar masoya kuma ya koyar da darusa da dama wato Dilwale Dulhania Le Jayenge yake bikin cika shekaru 25. Inda aka saki wannan fim a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 1995 inda a yanzu kimanin shekaru 25 kenan.
Fim ne da shahararren kamfaninnan wanda yayi fice a ƙasar ta India ya shirya shi wato kamfanin shirya fina-finai na Yash Raj, kuma haziƙin mai bayar da umarnin nanne ya bayar da umarnin fim ɗin wato Aditya Chopra. DDLJ fim ne da akayishi a ƙasashe guda 3 wato birnin London na ƙasar Ingila da ƙasar Switzerland da kuma ita kanta ƙasar ta India inda aka fara yin fim ɗin daga watan Satumba na shekarar 1994 zuwa watan August na shekarar 1995.
Wannan fim ya girgiza zuciyar masoya sosai, jarumi Shah Rukh Khan da jaruma Kajol ne suka haskaka a fim ɗin inda Shah Rukh Khan ya fito a mai suna Raj Malhotra inda itakuma Kajol ta fito a mai suna Simran Singh. Sauran juruman cikin fim ɗin sune Amrish Puri da Farida Jalal da Mandira Bedi da Karan Johar da Pooja Rufarel da dai sauransu.
Fim ne da ya nuna cewar Shah Rukh Khan da Kajol sun kamu da son junansu inda shikuma mahaifin Simran wato Kajol ya riga ya yiwa ɗan abokinsa alƙawarin cewar zai bashi ita alhalin kuma zuciyarta data Shah Rukh Khan ta narke a cikin kogin soyayya.
Dangane da bikin cikar wannan fim na Dilwale Dulhania Le Jayenge shekaru 25 jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta tattauna da haziƙar mai fashin baƙi gami da sharhi akan fina-finan Indiya dake jahar Kano wato Amina Abdurrahman Hassan dake unguwar Gama a unguwar Birget inda aka tambayeta game da cikar wannan fim shekaru 25 inda tace:
“To wannan fim na DDLJ yana ɗaya daga cikin fina-finan da jarumi Shah Rukh Khan da Kajol sukayi tare wanda ya taɓa zuciyar masoya kuma fim ne da yake nunin cewa idan wata damuwa ta sameka kokuma kaji kanason abu to babu makawa iyayenka ya kamata ka fara gayawa kamar yadda ita shi jarumi Shah Rukh Khan ya gayawa mahaifinsa ya kamu da son Kajol sannan itama dataji abin ya dameta itama ta gayawa mahaifanta”
Sannan jaridar dai ta sake tambayar Amina tunda wannan fim ɗin na soyayya ne ko wanne darasi yake nunawa ga masoya?
“To babban darasin da wannan fim yake nunawa ga masoya shine, lokacin da Shah Rukh Khan ya gayawa mahaifinsa cewar yanason Kajol ai kawai mahaifin cewa yayi tunda ka ganta kana sonta kawai kaje wajenta, kaga ana wannan fil ya koyawa masoya cewar idan kaga wata kanaso kokuma kikaga wani kinaso to ku bayyanawa juna domin idan baku bayyanawa juna ba to zaku shiga damuwa sosai kuma kuzo kuna da kunsani. Sannan wannan fim yana nuni da mace ko namiji su cire tsoron bayyana soyayyarsu ga wanda suke so kawai suje su bayyanamusu kai tsaye”.
Shidai wannan fim yayi nasara da dama a masana’antar ta Bollywood sannan kuma fim ne da ya lashe kyaututtuka kama daga kamfanin daya shirya shi da jaruman da suka taka rawar gani a cikinsa harma da mawaƙan da suka yi waƙoƙin cikin fim ɗin.
Fim ɗin dai ya mori waƙoƙi kamar haka:
1. Ghar Aaja Pardesi wadda Manpreet Kaur da Parmela Chopra sukayi.
2. Mere Khwabon Mein wadda mawaƙiya Lata Mangeshkar tayi.
3. Tujhe Dekha To wadda Kumar Sanu da Lata Mangeshkar sukayi.
4. Hoga Ya Hai Tujhko wadda Udit Narayan da Lata Mangeshkar sukayi.
5. Ruk Ja O Dil Deewane wadda Udit Narayan yayi.
6. Mehndi Laga Ke Rakhnna wadda Lata Mangeshkar da Udin Narayan suka yi.
7. Zara Sa Jhoom Loon Mein wadda Asha Bhosle da Abhijeet Battacharya suka yi.
Wannan fim na Dilwale Dulhania Le Jayenge yana ɗauke da mintina 189 wato kimanin awanni 3 da mintina 9 kenan. Sannan kuma wanda ya rubuta labarin wannan fil shine Aditya Chopra wanda shine ya bayar da umarnin fim ɗin kuma fim ne da baza a taɓa mantawa dashi ba.