A wannan rana ta Juma’a 30 ga watan Oktoba za a fara fafata gasar share face mai taken Masari Pre-Season Tournament wadda za a gudanar a jahar Katsina kenan.
Za a dinga fafata wasannin a filin wasa na Katsinan Dikko dake cikin birnin na Katsina, sannan kuma za a kwashe wasu kwanaki ana gudanar da gasar.
A uammacin jiya Alhamis aka fitar da jerin rukuni gida biyu wato rukunin A da B.
Ga jerin yadda aka fitar da rukunan kamar haka:
RUKUNON A:
Sokoto United.
Niger Tornadoes.
Katsina United A.
Plateau United
Garkuwa Fc
Junior Katsina United.
RUKUNIN B:
Kano Pillars.
Wikki Tourists.
Katsina United B.
Zamfara United
Rarara Academy
Danburam FC
Dadinkowa FC
A yau Juma’a za a fafata wasanni kamar haka:
Junior Katsina United da Garkuwa FC.
Katsina United A da Dadinkowa FC.
Katsina United B Niger Tornadoes.
A rana ta biyu kuwa wato gobe Asabar.
Kano Pillars da Dadinkowa FC.
Garkuwa da VS Sokoto United.
Rarara da Damburam FC.
Katsina United B da Zamfara United.
A ranar Lahadi kuwa:
Dadinkowa da VS Rarara Academy
Danburam da Zamfara United.
Katsina United A da Sokoto United.
Plateau United da Niger Tornadoes.
A rana ta huɗu wato ranar Litinin.
Zamfara da Rarara Academy.
Sokoto United da Katsina United A.
Garkuwa da Plateau United.
Katsina United B da Wikki Tourists.