Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce yana goyon bayan dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Idan ba amanta ba, Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov na karamar hukumar Gboko a jihar Benue, ya dakatar da Ayu a ranar Lahadi, bayan da aka kada masa kuri’ar yankan kauna kan wasu ayyukan da yayi kuma ake zargin zagon kasa ne ga jam’iyyar ta PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Wasu Mata Na Zanga-Zanga Tsirara Ofishin Jakadancin Amurika
Da yake magana kan wannan batu, Wike wanda ya kasance bako a wani shiri na gidan talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily ya bayyana cewa yana goyon bayan matakin ne saboda Ayu ya taka rawa sosai wajen rashin nasarar PDP a zaben 2023.
Gwamna Wike ya ce masu ruwa da tsaki da ke da muradin PDP a zuciya, ba za su iya zama suna kallon yadda ake lalata ta a hannun mutanen da ba su da alaka da jam’iyyar.
Ya kara da cewa, babu wanda zai karbar umarni daga dan siyasar da ba zai iya kai kawowa jam’iyarsa nasara a yankinsa ba.
A wani labarin kuma, Yadda Ake Zargin Wani Fasto Da Yin Lalata Da ‘Yar Majami’arsa Mai Shekara 17 – Likita
Wata Likita, Misis Maria Fadaka, a ranar Litinin ta shaida wa wata Kotun kula da laifukan Jima’i da cin zarafin Jama’a a Ikeja, yadda take zargin wani Fasto, Chris Mcdouglas, ya yi lalata da wata ‘yar wata Cocinsa mai shekara 17.
Mcdouglas, wani Fasto a Cocin Peculiar Generation Assembly, da ke Legas, yana fuskantar tuhuma tara da suka hada da lalata da kuma cin zarafi ta hanyar tilastawa