Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, a ranar Litinin ya gargadi mambobin jam’iyyar da su guji yi aiyukan da ba su dace ba, yana mai cewa ba za a bar su su yi tafiya haka kawai ba saka-ka ba.
Ya yi wannan gargadin ne a Abuja a jawabinsa na bude taron masu ruwa da tsaki da kuma kaddamar da kwamitin sulhu kan zaben gwamnan jihar Ekiti.
Taron wanda kwamitin ayyuka na kasa ya kira ya samu halartar shugaban kwamitin amintattu Sanata Walid Jibrin; shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, Gwamna Nyesom Wike; Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, da kuma tsohon Gwamna Ayo Fayose.
Haka kuma akwai masu neman takarar gwamna 17 a jihar Ekiti da suka hada da Segun Oni, Olusola Eleka, Sanata Abiodun Olujinmi, da Ajijola Lateef Oladimeji da dai sauransu.
Ayu ya ce majalissar zastaswa ta jam’iyar NWC ta dauki muhimmin mataki na fara wannan tsari na warware matsalolin da ke faruwa a sassan jihohin kasar nan, domin a samu hadin kai da kuma wuce tsara wajen shiga kowane zabe, ciki har da zaben shugaban kasa da na sauran zabukan da ke tafe a 2023.