By Abbas Yakubu Yaura
Zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya musanta zargin shirin da gwamnatinsa take yi na gudanar da bincike a kan tsofaffin magabatan jam’iyyar wadanda suka jagorance ta abaya.
Ayu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa dake Abuja ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Ayu, wanda tsohon shugaban majalisar dattawa ne, ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a watan Oktoba domin ya gaji kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Uche Secondus kuma ana sa ran za a ci gaba da aiki tare da sauran mambobin NWC a ranar 9 ga watan Disamba, 2021.
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Okwesilezie Nwodo, yace a cikin wata takarda mai suna ‘kafa jam’iyar siyasa’, wacce ya gabatar a yayin taron kwana biyu na kasa da aka gudanar wa sabbin zababbun mambobin NWC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abuja ranar Alhamis, ya bukaci. jam’iyyar ta sa ido sosai kan asusun ajiyarta sakamakon rashin gaskiya a harkokin tafiyar da kudaden ta da gwamnatocin da suka shude suka yi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ayu yayin da yake mayar da martani yace gwamnatinsa za ta sake duba rahotannin kwamitoci daban-daban da hukumar NWC mai barin gado ta kafa, ta duba gaskiyar lamarin tare da magance kowace matsala bisa ga gaskiyar da ake da ita.
“Hukumar NWC mai barin gado ta kafa kwamitoci daban-daban domin duba fannoni daban-daban, zamu tattara duk rahotannin, sannan mu sake duba su, mu duba gaskiyar kuma mu halarci kowane batu bisa ga gaskiyar da muke da ita.Ina so in tabbatar muku da cewa za mu yi kokarin tsaftace gidanmu ko da wanene zai shafa.
Sai dai zababben shugaban jam’iyyar na kasa a wata sanarwa da ya fitar daga ofishin yada labaransa, yace bai ga littattafan jam’iyyar ba, kuma ba zai iya yin tsokaci mai karfi kan duk wani zargi ba, yana mai cewa yana aiki da gaskiya.