A tarihin jihar Kaduna ba a taba yin wata hukuma mai zaluntar talakawa irin KASTELIA ba. Yanzu takai ga cewa babu dama talaka ya fita da babur din sa dan bidar halaliyar sa ba tare da fargabar haduwa da wadan nan jami’ai da suka kware wajen zaluntar al’umma ba.
Yau masu motoci kullum suna cikin zullumi tare da faduwar gaba in suna tuki a kan titunan jihar Kaduna ko da kuwa ba su da laifi dan sun San sai an bata masu lokaci.
Ita wannan hukuma an kafata ne domin kare hadura da kuma hana Go-slow a titunan jihar Kaduna amma abin takaici, yanzu ban da hada hadura, gallazawa talakawa tare da kuma hada jerin gwano na motoci babu abin da suke yi.
Muna kira da babban murya, ga gwamnatin jihar Kaduna ta kawo gyara a wannan hukuma kafin irin gallaza wa al’umma da wannan hukuma take yi ya sa ayi mata bori.