Rabaran Ignatius Kaigama na Cocin Catholic Archdiocese dake birnin tarayya Abuja ya shawarci shugabannin Nijeriya da kuma jami’an gwamnati da su yi amfani da lokacin sabuwar shekara su tuba ya zuwa ga Allah su daina ayyukan almundahana da alfasha.
Rabaran Kaigama ya bayyana hakan ne a sakon na sabuwar shekara a Abuja a ranar Alhamis. Inda ya kara da cewa; wadanda suke rashawa da almubazaranci da kudaden gwamnati su duba su koma ga Allah, domin a cewarsa daina hakan zai fitar da Talakawa daga kangin Talaucin da suka shiga.
Rabaran Kaigama ya ce akwai bukatar kawo sauyi a kasarnan idan har ana son ci gaba mai amfani.