Jami’an ‘yan sandan Edo sun karyata batun yunkurin fashi a ofishin babban Bankin Nijeriya, CBN dake garin Benin.
DCP Ayoola Ajala, Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da samame, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Talata, inda ya ce; ba gaskiya bane cewa an yi yunkurin fashi a bankin.
Ya tabbatar da cewa; lamarin da ya auku shi ne; an kori wadansu ‘yan kungiyar asiri ne a yankin, wadanda suka gudu ta titin Akpakpava inda Bankin CBN din yake.
Ajala, har wala yau biyu daga cikin ‘yan kungiyar asirin an cafke su. A yayin da sauran kuma suka tsere. Ya tabbatar da cewa an cafke wadansu makamai daga hannun ‘yan kungiyar asirin.