Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi raddi mai zafi kan kalaman da abokiyar hamayyarta mai mulki wato APC da ta yi wacce take nuni da cewa sai ta kwashe shekara 36 tana mulkin Nijeriya.
Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban jam’iyyar ta APC na riko shi ne ya bayyana kudurin APC din a jiya Talata.
Sai dai Kakakin PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya ce ikirarin da APC ta yi na sabunta rijistar zabe ta ‘yan kasar miliyan 36, karya ce kawai sannan babu wani tasiri da hakan zai yi ga ‘yan Nijeriya.
Sannan ya yi nuni da cewa; ‘yan Nijeriya sun shirya tsaf domin fatattakar jam’iyyar APC a shekarar 2023. Sannan ya tabbatar da cewa su ba su tsorata da dukkanin ikirarin APC ba. A don haka ya ce Kalaman Mai Mala Buni ba za su yi tasiri ba, domin a cewarsa ‘yan Nijeriya ba za su zuba ido su ci gaba da rayuwa cikin kunci ba har na tsawon shekara 36 ba.