Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC tace ‘yan takarar jam’iyyun siyasa da suka mallaki jabun shaidar karatu a babban zaben 2023, hukumar zata hada hannu da hukumomin dake yaki da hakan domin ganin sun fuskanci hukunci.
A cewar hukumar Irin wannan hadin gwiwa, zai hada da hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka da kuma hukumar kula da da’ar ma’aikata.
INEC ta kuma bayyana cewa babu wata takamaiman doka da ta tilasta wa ‘yan takarar zabe gabatar da shaidar biyan haraji kafin su iya tsayawa takara.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a Abuja, yayin wani taro kan hadin gwiwar masu rike da mukaman siyasa, wanda aka kira a hadin gwiwa da hukumar haraji.
Sauran hukumomin da suka bayyana a yayin taron sun hada da manyan jami’an hukumar tara haraji ta kasa da kuma hukumar kula da da’ar Ma’aikata.
Yakubu ya ce bayan soke zaben ‘yan takarar da suka gabatar da takardun bogi ko na jabu, ya yi imanin cewa ya kamata a gurfanar da irin wadannan mutane a gaban kuliya.