Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) a kasar nan sun bayyana cewa ba dukkan na’urorin lantarki da gwamnatin tarayya ta amince da su ba ne kyauta ga kwastomomin su.
Kamfanin DisCos a cikin wata sanarwa da kungiyar dillalan wutar lantarki ta kasa ANED ta fitar a jiya, ta bayyana cewa akwai tsare-tsare na auna mitoci daban-daban da gwamnati ta sanya kuma biyan kudin mitoci ya ta’allaka ne da tsarin da abokin ciniki ke shiga.
Babban Daraktan ANED, sashin Bincike da Shawarwari, Barr. Sunny Oduntan ya bayyana cewa “a karkashin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ‘Samar da kadarorin Mita da Dokokin Mitar Jama’a na Kasa’, Doka mai lamba NERC-R-11-2021, akwai shirye-shirye guda biyu na mitoci.
“NMMP tsari ne na gwamnatin tarayya, tare da tallafin babban bankin Najeriya (CBN). An fara wannan shirin ne a shekarar 2021 kuma makasudin shirin shine a gaggauta rufe gibin auna wutar lantarki. Ana ba da waɗannan mitoci kyauta ga abokan ciniki kuma a matsayin lamuni ga kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos).
“Kashi na farko na NMMP ya shafi isar da kayan aiki da shigar da mita miliyan kuma an kammala shi a watan Oktoba, 2021. A kashi na biyu, ana sa ran za a girka karin mita miliyan hudu.”
Mista Oduntan ya kuma kara da cewa “Hanya ta biyu wajen samun mitar tana karkashin tsarin samar da kadarorin Mita (MAP) wanda aka amince da shi a shekarar 2018. Wannan hanyar tana samuwa ga kwastomomin da ba sa son jiran samar da mitoci a karkashin NMMP. Irin waɗannan abokan ciniki na iya biyan mita ɗaya a ƙarƙashin tsarin. Adadin da abokin ciniki ya biya za a gyara shi kuma a mayar da shi cikin watanni 36 ta hanyar kiredit na makamashi.
Abin lura shine cewa a ƙarƙashin shirin na biyu, tare da fa’idar saurin bayarwa da shigarwa, abokin ciniki dole ne ya fara biyan kuɗin mita kafin a dawo da shi. Daga ƙarshe, mitar za ta iya zama kyauta ga abokin ciniki, ta hanyar ƙimar kuzari.