Mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi Kanal Sama’ila Yombe (mai ritaya) a ranar Alhamis ya musanta jita-jitar dake cewa an sace shi, a yayinda tawagar shi, ƴan bindiga suka kai hari, a lokacin da ya ziyarci Sojoji a yankunan dake fama da matsalar tsaro a Kudancin Jahar.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Jaridar Daily Trust a Birnin Kebbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babban Taron APC: Abubakar Sani Bello ya kira taron gaggawa
Ya ziyarci yankunan dake fama da matsalar akan abinda ya bayyana a matsayin ‘ziyarar Sojoji a fagen daga’ domin duba yanayin yadda ake yaƙin, da kuɗaɗe, gami da kayayyakin sojin.
Kanal Yombe ya bayyana cewa ya bi Kwamanda zuwa yankunan, domin duba yadda suke gudanar da yaƙin.
Ya ƙara dacewa, ƴan bindigar wanda suka saje da Mazauna garin Kanya, sun kai hari ga Sojojin, wanda ya sanya aka yi musayar wuta a ƙauyen.
Akan yawan mutanen da suka ji raunuka, Yombe yace ba’a bashi damar faɗin adadin mutanen da suka jikkata a lokacin musayar wutar.