Tsohon Shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar Mai Ritaya, ya ce atafau ba jirgin shi aka kama yana safarar abinci da makamai wa yan bindiga ba, hasalima bai san mai jirgin ba.
Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya ce wannan labari abin bakin ciki ne, abin kuma takaici a dangantasa da shi.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce lashakka wannan batu an kago shi me don kara rura wutar fitina da take addabar kasar nan.
Kazalika ya ce ya yi matuƙar mamakin yadda mutane za su zauna su sharara karya wa jama’a don kawai su bata wa wani suna da kima a idon duniya.
Daga bisani sai ya ja hankalin yan kasa da su guji irin wadannan munanan labarai, tare da yin kaffa-kaffa wajen yaɗa su musamman a shafukan sada zumunta na zamani.