Ba ka da cikakkiyar lafiya – Pat Utomi ya ƙalubalanci Tinubu kan bayyana gwajin lafiyar sa ga jama’a
Wani jigo a jam’iyyar Labour kuma masanin tattalin arziki a siyasance, Pat Utomi, ya kalubalanci dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, da ya je a duba lafiyarsa, sannan ya bayyana sakamakon.
Ya yi ikirarin cewa Tinubu bai dace ba, bashi da lafiya.
Farfesa Utomi ya jefa kalubalen ne a ranar Litinin yayin da yake amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV’s Politics Today, inda ya ce zaben badi ya shafi rayuwar ‘yan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Karnuka Na Kashe Ƴan Najeriya 55,000 A Duk Shekara – USAID
Ya ci gaba da cewa akwai alamun da ke nuna cewa Tinubu bai cancanci mukamin shugaban kasa ba.
“Kasarmu ta sha wahala sosai saboda samun shugabanni marasa lafiya. Don haka ne mataimakin shugaban kasar ya tashi.
“Shugabannin Amurka suna yin gwajin lafiya su bayyana ga jama’a. A bar shi (Tinubu) ya je neman magani tare da likitocin Najeriya a asibiti sai a bayyana sakamakon.
Utomi ya kara da cewa “rayuwar miliyoyin mutane ne muke hulda da su.”
Shahararren masanin tattalin arzikin ya kuma bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi kuskure da rashin fitar da wani dan takara a matsayin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, inda ya ce da ya fi cancanta.
“Da ma mataimakin shugaban kasa (Yemi) ya kasance mutumin da ya dace. Za ka ga shi (Tinubu) ba shi da lafiya. Na kowa, kada mu kashe kanmu, mu fadi gaskiya,” in ji shi.
A wani labarin kuma: Kana da Kyawan Ɗabi’u da Biyayya — Buhari ya yi Ta’aziyyar Tsohon Shugaban NIMASA Fashakin
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyana alhininsa game da rasuwar tsohon babban daraktan hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, Rotimi Fashakin.
Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya ce: “A matsayin tsohon kakakin jam’iyyar CPC, ina alfahari da cewa Fashakin ya kasance daya daga cikin jajirtattun jam’iyyar da na taba sani da alaka da su.”