Ba kada mahimmanci a siyasance, ka janyo wa PDP shan kaye a 2015 – Wike ga Lamido
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya mayar wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido martani, inda ya ce ya rasa ‘yancinsa a siyasance.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC Ta Kama Akantan Hukumar NDDC Kan Badakalar Naira Billiyan 25
Lamido a ranar Talatar da ta gabata yayin da yake magana a gidan Talabijin a shirin siyasar mu a yau, ya ce babu bukatar sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, inda ya ce babu wanda ya zalunce gwamnan Rivers.
Sai dai Wike, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana kalaman Lamido a matsayin abin kyama, inda ya kara da cewa shi da tawagarsa sun shagaltu da haifar da rikici da bangaranci.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun lura da kalaman batanci da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi game da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, a wata hira da ya yi a gidan Talabijin na Channels kwanan nan.
“Duk da cewa, ba za mu iya musanta cewa Lamido na da wani hakki na ra’ayinsa ba, muna so mu bayyana cewa, duk da haka, ba shi da ‘yancin yin zagon kasa ga gwamna Wike, wanda ba a cece-ku-ce a kan dimbin gudunmawar da jam’iyyar PDP ta bayar.
“Abin takaici ne a daidai lokacin da masu son bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya da hadin kan jam’iyyar ke kokarin ganin an warware wasu rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar PDP, Lamido da ‘yan uwansa, wadanda tun daga lokacin suka rasa nasaba da siyasa, sun shagaltu da haifar da rikici da tsangwama.”
“Watakila, Alhaji Lamido yana tunanin ‘yan Najeriya na fama da wasu zababbun afuwar da suka manta cikin gaggawa, irin rawar da shi da ‘yan kungiyarsa suka taka a tsakanin 2014 zuwa 2015, wanda ya kai ga kayar da PDP a zaben 2015.”
A WANI LABARIN KUMA:Dole Jama’a su taimakawa hukumomin tsaro – Soji