• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Sunday, April 2, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

Ba Kwadayin Mulki Ya Sa Na Ke Goyon Bayan Sanata Lawan Da Gbajabiamila Ba –Tinubu

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
April 24, 2019
in Labarai
Reading Time: 7 mins read
1 0
0
1
SHARES
11
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Tunde Rahman

“Mu na bibiyar labarai da ake ta bugawa barkatai, cewa wai Asiwaju Bola Tinubu ya na kokarin yin karfa-karfa a tsarin zaben Shugabannin Majalisar Tarayya. Labarai na soki-burutsu na nuna cewa Asiwaju na ta gaganiyar yin gaban-gabarar dora shugabannin domin ya share wa kan sa hanyar zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

“Baya ga cewa wadannan labarai da rahotanni duk karairayi ne, masu watsa wadannan maganganu su na kuma kokarin kawo nakasu wajen kokarin da Shugaba Buhari ke yi domin yi wa Najeriya kyakkaywan garambawul. Saboda haka, ganin ana neman a shiga hurumin kokarin da Buhari ke yi mu ka ga ya dace mu yi magana. Amma ba don haka ba, sai mu ci gaba da kallon abin da ke faruwa mu na yi musu dariya kawai.

“Ba da dadewa ba fa Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC suka samu nasarar sake lashe zabe. A yanzu Shugaba Buhari zai fara shirin jagorantar kasar nan zuwa zangon sa na biyu, tsawon wasu shekaru hudu. Musamman tunda an yi sa’ar Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya duk APC ce ke da rinjaye. Amma maimakon a rika maida hankali wajen ajandar Shugaba Buhari ta ‘Next Level’, tuni masu azarbabi har ma sun tsallake gaba su na batun zaben 2023, tun Buhari bai ma fara zangon san a biyu ba.

“To sai dai akwai bukatar yin la’akari da cewa su fa ’Yan Najeriya ba su zaben ’yan siyasa su zura ido su na kallo ana ta kwatagwangwamar neman kukami a zabe na gaba. Mutane na zaben wadanda suka yi amanna cewa za su yi aiki tukuru domin ciyar da kasa da al’umma a gaba. Dalili kenan suka sake zaben Shugaba Buhari, suka yi fatali da gungun ’yan hauragiyar cikin PDP.

“Abin mamaki, su masu watsa wannan ji-ta-ji-ta a kan har ma sun rigaya sun shiga cikin zuciyar sa sun san abin da shi bai ma sani ba. Kai jama’a!

“Saboda azarbabi har sun tsallake zango na biyu da za a shiga, ba su ma yin maganar sa, sun tsallaka cikin 20123. Ina ma a ce irin wadannan ’yan jagalisa sun yi amfani da fasahar su ta kirkairar karya, sun koma su na yi wa kasar su aiki. Hakan zai fi wannan ji-ta-ji-ta da da gulmammakin da suka rika kitsawa.

“Wannan kokari da ake ta yi wajen shafa masa bakin fenti a nuna dukkan kokarin da ya ke yi duk tuggun neman mulki ne, ba zai yi nasara ba. Saboda ba gaskiya ba ne. Kanun labaran da ake ta watsawa cike suke da karairayi da kuma rashin tunani, saboda babu hujjoji ko kadan a cikin su. Tun da Asiwaju ya kammala wa’adin shekarun sa takwas na Gwamnan Jihar Lagos cikin 2003, har yau bai sake tsayawa takarar wani mukami ba, bai kuma taba neman a ba shi wani mukami ba. Don haka ko shugabancin jam’iyyar APC bai taba nema ba.

“Idan aka ce mutum ya fadi sunan wani fitaccen dan siyasa wanda har yanzu ake damawa da shi, amma kuma har yau bai nemi a ba shi wani mukami ko sake fitowa takarar wani mukami ba, to ban ce babu ba, amma dai da wahala a samu kamar Asiwaju.

“Yayin da akasarin ‘yan siyasa da sun sauka daga mulki kuma sai su kama gaganiyar neman wani mulki ko matsayi, shi kuwa Asiwaju sai ya ajiye son zuciyar sa, shi ya sa sai dai ka ga wasu makusantan sa ko abokan tafiyar sa ne ke tafiya tare da ra’ayoyin sa da akidun sa na siyasa.

“Wannan halayya kuwa ai ba irin ta mutumin da ke neman mulki ba ne bagatatan. Yayin da masu baza wannan tuggun na kokari su nuna Asiwaju a matsayin mutum mai matsanancin kwadayin mulki, sai ga shi ayyukan da ya ke yi sun nuna akasin haka. Masu baza wannan tatsuniyar son mulki ga Asiwaju, ba su san iyar zurfin ruwan sa ba, kuma ba su san abin da ke sa shi zage damtse ya na gudanar da sha’anin sa na siyasa cikin kuzari ba. Sai kawai suka yi masa ta su fassarar daban, kuma suke nuna wa duniya wai yadda suke fassara shi, to haka din ya ke.

“Sai ga shi wadannan ji-ta-jta da su ke watsawa ta fallasa miyagun halayen masu baza su, maimakon su fayyace yadda halayyar Asiwaju ta ke. Hakan ya rika nuna irin yadda masu baza karairayin za su yi idan da su ne Asiwaju. Saboda ba su da wata fikira ko fasaha da basirar kawo ci gaba ko shawarwarin da za a magance wata matsala, ko warware kalubale, sai kwakwalwar su da tunanin su ya karkata wajen kitsa tuggu da kutunguilar siyasa kawai.

“Shi fa Asiwaju tun da ya bar ofis a cikin 2003, sai ya maida hankali wajen kafa jam’iyya da kuma gina ta har ta yi nasara, ta yadda za ta yi yalwar da za ta maye gurbin PDP, jam’iyyar maida al’umma koma-baya.

“Shi ya sa aka ga ya taimaka wa APC wajen hada hannu da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ke da kyakkyawar akidar siyasa irin ta sa. Tun daga lokacin da ya shiga siyasa, Asiwaju ya maida hankalin sa wajen taimaka wa Shugaba Buhari ya gudanar da kudirorin sa wadanda za su bai wa kowane dan Najeriya damar samun albarkar da zai wadatar da iyalin sa.

“Yayin da ya ke shirye-shiryen shiga zangon sa na biyu, Shugaba Buhari ya furta cewa zai bada karfi da fifiko wajen inganta tattalin arzikin kasa. Wadannan kudirorin muhimmai ne kuma tilas ta haka ne za a iya ciyar da Najeriya gaba. Sai kuma kalubale da shingayen da ke gaban mu su na da yawa, kuma tsallake su sai mun yi da gaske.

“A kwakwalwar sa da zuciyar sa da kokarin sa, Asiwaju ya maida himma ne kacokan wajen ganin ya na taimaka wa shugaban kasa domin ya kai ga nasarar inganta tattalin kasa. Kuma dama irin wannan ra’ayin ne shi ma Asiwaju ya ke da shi.

“Saboda irin yadda tafiyar a yanzu ta samu kan ta cikin wani mawuyacin hali, dalili kenan Asiwaju ya ki kauda kan sa daga ganin an gyara matsalar da ke gaban mu a yanzu. Domin sai yau ta yi kyau ake samun kyakkyawar gobe.

“To a kan haka ne za a kalli matsayar da ta sa Asiwaju ya goya wa wasu baya domin su kasance shugabannin Majalisar Tarayya. Kuma a haka za a fassara nufin sa da fahimtar sa. Ashe kenan ba za a yi mamaki ba don ya goyi bayan matsayar da Shugaban Kasa da kuma jam’iyyar APC suka dauka. Kuma hakan da ya yi ba laifi ko aibi ba ne. A matsayin Asiwaju na dan jam’iyya mai kuma yi wa jam’iyya biyayya, zai yi babban kuskure idan ya kauce daga turbar da shugaban kasa da jam’iyya ke so a bi.

“Mun dai san irin muhimmancin da mukamin Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya ke da shi wajen ganin Shugaban Kasa ya cimma kudirorin da ya ke son cimma. Ya kamata mutum ya kalli shekaru hudun da aka shafe sannan ya dubi darasin da aka koya daga abubuwan da suka rika faruwa, inda shugabannin Majalisar Dattawa suka rika zame wa shugaban kasa da gwamnati karfen-kafa, alakakai tare da yi wa harkokin tafiyar da gwamnati kafar-ungulu.

“Ku dubi dai yadda Saraki da Dogara da ’yan amshin-Shatan su suka rike wa kasafin kudi makogaro tsawon shekaru hudu. Sun rika kin sakin kasafin kudi, kuma suka rika cusa ayyukan su wadanda za su rika kudancewa a rana daya daga cikin kudaden gudanar da ayyukan.

“Abin na su ya yi munin da har kudaden da za a yi wa al’umma ayyukan ci gaba suka rika zabtarewa. Saboda haka bayan mun shafe shekara takwas su na hana ruwa gudu, ya kamata mu yi duk irin abin da za mu iya domin kauce wa maimaita fadawa hannun Shugabannin Majalisar da suka rika hana ruwa gudu tsawon shekaru hudu.

“Wannan kudirin ne kadai Asiwaju ke so ya cimma, amma ba wata boyayyar manufa ya ke da ita ba. Duk wani abin da ya ke yi, da sani da kuma fatan Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC.

“Saboda haka masu jefa wa Asiwaju bakaken maganganu, to a zahiri Shugaba Buhari ku ke gwasalewa, domin da matsayi daya ya dauka da Asiwaju. A dimokradiyya kowa na da ’yancin ya soki ra’ayin da suke so su yi suka a kan sa. Amma fa idan masu baza wannan ji-ta-ji-ta shugaban kasa suke so su kalubalanta, to su daina fakewa da guzuma su ka harbin karsana. Su fito fili su yi suka ga Shugaban Kasa kai tsaye.

“Abin da duk wani wanda ya damu da kishin Najeriya zai yi a yanzu, shi ne ya goya wa shugaban kasa baya domin ganin ya cimma burin sa na tabbatar da nasarar manufafin sa na tattalin arzikin kasa. Ta haka ne za mu iya ci gaba a matsayin mu na neman zama kasaitacciyar kasa.

“A karshe, ya kamata masu yada wannan ji-ta-ji-ta su gane cewa kwanan nan Asiwaju ya ce babu wani hobbasa da wani zai yi a yanzu da zai iya tunanin idan ma ya yi zai iya samun garanti na cimma wata manufar siyasa nan da shekaru hudu masu zuwa. Kenan zance ne na marasa tunani har wasu su ruka cewa idan wani ya na da kusanci da shugabannin Majalisar Tarayya, hakan zai iya karfafa yunkurin sa na neman takarar shugabancin kasa.

“Cikin 2015 Sanata Saraki ya kitsa kitimirmirar da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa. Amma hakan da ya yi, ya nuna shi mutum ne maras kishin talakawan kasar nan. Mulki da mukami ne kawai a gaban sa. To a yanzu dai ya kusa barin wadannan ababen da ya ke kwadayi. Har gara ma Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, a iya cewa da dan dama-dama. Samun mukami ba garanti ba ne na samun nasara a can gaba.

“Ita fa siyasa ta na bukatar kulle-kullen yadda za a zakulo mutanen da suka cancanta domin dora su a mukaman da su ne suka cancanta. Domin samun wannan nasarar mu ke ta kokarin saisaita siyasar ta yadda Shugaba Buhari zai kai ga samun nasarori a kudirorin inganta tattalin arzikin kasa da ya ke kokarin cimma aiwatarwa. Wannan ne kadai bukatar Asiwaju ba wani abu ko wata manufa ta daban ba.

“Yanzu dai zabe ya zo karshe. Abu mafi muhimmanci shi ne mu bada goyon bayan ganin gwamnati ta zauna daram yadda za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta sa a gaba.

Wadanda ke ta kulla kutunguilar 2023 kuma sun nuna kan su a fili cewa ba ci gaban jama’a ne a gaban su ba. Kuma babu ruwan su da kalubalen da kasar ke fuskanta. Ba mu da wani lokacin da za mu bata a yanzu da har da za mu rika mafarkin abin da zai faru can gaba. Abin da ke gaban mu a yanzu shi ne abin da ya shafe mu.

“Shi dai Asiwaju abin da kawai ya sa a gaba shi ne tabbatar da ci gaba da ingantacciyar gwamnati sai kuma kokarin warware kalubalen da ake fuskanta a yau. Ba shi da wani ko wata boyayyar manufa.

Wadanda ke ta bata wa kan su lokaci su na kitsa karairayi, gulma da tuggu a kan sa, zai fi kyau su taimaka wa kan su da kuma kasar nan, su daina sannan su koyi da bin turbar nagartacciyar siyasar Asiwaju.

RAHMAN Shi Ne Kakakin Yada Labarai Na Asiwaju Bola Tinubu.

Tags: tinibu
Previous Post

Sabon Salon Yin Garkuwa Da Mutane, A Jihar Kano

Next Post

Shin ya dace a baiwa mai auri saki mata? Wani lokaci akwai gangancin iyaye wajen jefa ya’yan su wajen mazaje baragurbi

Next Post

Shin ya dace a baiwa mai auri saki mata? Wani lokaci akwai gangancin iyaye wajen jefa ya'yan su wajen mazaje baragurbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2507 shares
    Share 1003 Tweet 627
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2279 shares
    Share 912 Tweet 570
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2051 shares
    Share 820 Tweet 513
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1766 shares
    Share 706 Tweet 442
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1390 shares
    Share 556 Tweet 348
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

April 2, 2023
Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

April 2, 2023
Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

April 1, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
Labarai

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
Labarai

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8
Labarai

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
  • Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
  • Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In