Labarin tsige gwamnan Jahar Plateau Simon Lalong ya karade kafafen watsa labarai a cikin kwana-kwanannan, sai dai dan majalisa Rt. Hon. Abok Ayuba, yace wannan zancen kanzon kurege ne.
Kamar yadda Rt. Hon. Abok Ayuba, yake cewa “a matsayin mu na wakilan jama’a muna cikin damuwa kan tashin hankali da kashe-kashe dake faruwa a Jahar, ya kamata gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai da suka dace.”
Ya cigaba da cewa “Gwamna Lalong mutum ne wanda Yan majalisun suna matukar ganin girman sa, kuma ba sa da wani nufi na tsige shi.”
A WANI LABARIN:- EFCC ta kama masu Damfara ta yanar gizo 15 a jihar Abia
” Simon Lalong shine gwamnan Jahar Plateau wanda mutane suka zaba da kansu, haka muma Yan majalisu muna goyan bayansa har sai ya kammala wa’adin mulkinsa.”
Idan baku manta ba Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito maku kan yadda batun tsige gwamna yake ta yaduwa a kafafen sada zumunta.
Abok Ayuba yace gwamna Lalong mutum ne Mai karbar shawara kuma yanzu haka ya fara daukan matakai kan yadda za’a dakile aukuwar lamarin nan gaba.
“Kamar yadda kuke gani, gwamna Lalong ya Ziyarci wuraren da abubuwan suka auku a garin Yelwa Zangan.”
Daga karshe Rt. Hon. Abok Ayuba, yace Yan majalisun za su hada karfi da karfe da gwamnan don ganin an samar da dawwamammen zaman lafiya a Jahar.