Daga Mukhtar Yakubu.
An dade ana ta rade raden cewar, fitaccen Furodusa kuma jarumi Lawan Ahmad, ya na karbar kudade a wajen duk wani jarumin da ya ke so a saka shi a cikin fitaccen fim din nan mai dogon zango na Izzar so.
Maganar ba tun yanzu ta ke yawo a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, inda a ke fadar cewar, Lawan Ahmad ya mayar da fim din Izzar so wata hanyar samun kudi, a wajen duk wani jarumin da ya ke son ya fito a cikin fim din, a maimakon a biya shi kudin aikin sa, da ya yi, to shi ne ma zai biya wasu kudi masu yawa.
Wannan ne ya sa wakilin jaridar Dimokuradiyya ya ji ta bakin Lawan Ahmad kan maganar, inda ya shaida mana cewar “Maganar wai ina karbar kudi don mu saka jarumi a cikin fim din Izzar so ba gaskiya ba ce, don mu ne ma mu ke biyan mutum idan ya yi mana aikin, yanayin aikin ka yanayin hakkin ka da za mu ba ka, don haka babu maganar muna karbar kudi.” a cewar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nnamdi Kanu da Sunday Igboho zasu Sami yanci~ wani Pastor ya musu alkari
Wakilin na mu ya Kuma kara tambayar shi, ko dai akwai wani tsari makamancin hakan da ya sa a ke yada wannan maganar?
Sai ya ce” To ni dai ban sani ba. Amma dai mutane su sani, kamfanin mu yana da tsari kamar sauran kamfanoni, wannan ya sa, muna da tsarin duk wani jarumin da ya ke son ya yi aiki a Kamfanin mu, to sai ya sayi fom ya yi rajista da kamfanin mu, don haka akwai fom da mu ke sayarwa dubu biyar, wanda in dai mutum zai kasance a karkashin kamfanin mu sai ya cike wannan fom din, in ban da shi to babu wani kudi da mu ke karba a wajen jarumai. “Inji shi.
Daga karshe ya yi kira ga sauran takwarorin aikin na shi, a matsayin su na yan fim masu sana’a daya, da su hada kan su ba wai aje ana yada jita jita ba.
Comments 2