Kungiyar nan ta yan binda a yankin Inyamurai wato IPOB wacce kuma ta yi kaurin suna a yan baya-bayan nan wajen kai hare wa ɗaiɗaikun mutane gami da kadarorin gwamnati, ta nesanta kanta da kisar tsohon mai baiwa Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmad Gulak.
A jiya ne dai aka hallaka Gulak jim kaɗan bayan ya bari wani otal dake birnin Owerri zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Mbakwe dake Jihar Imo.
Kisar da aka alakanta da kungiyar yan bindigar Inyamurai, la’akari da dokar da shugabanta Nnamdi Kanu ya bayar na cewa kada kowa ya fita.
To sai dai kakakin kungiyar Emma Powerful ya musanta wannan zargi inda ya ce kwararrun yan ta’adda ne suka aikata irin wannan aika-aika ba wai IPOB ba.