Fadar shugaban kasa ta ce ba ta da masaniya kan matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na bai wa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele hutu domin yaje karatu. Kamar yadda Daily Trust Ta ruwaito.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin Daily a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi A Wata Shahararriya Kasuwa A Jihar Oyo
Ya ce matsayinsa kamar yadda wata jaridar kasar nan ta ruwaito a safiyar ranar Asabar bai canza ba.
A baya mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana cewa: “Idan har gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya samu hutu domin zuwa ya karo karatu da ake zaton shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sahale masa, to ba mu san da hakan ba..
Wata kafar yada labarai ta yanar gizo, mai suna SaharaReporters, ta ce shugaba Buhari ya ba Gwamnan CBN hutu domin ya karo karatu, wanda hakan zai sa ya gudu daga Najeriya kafin bikin rantsar da zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya kara da cewa damar da Emefiele ya samu na ficewa daga kasar kafin Buhari ya sauka daga mulki na zuwa ne a daidai lokacin da ake zarginsa da cin hanci da rashawa da kuma tallafawa Yan ta’adda da kudade.
Kafar yada labaran ta yanar gizo ta ce jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS, wadda ta yi yunkurin kama Emefiele tare da tsare shi a baya, ba ta ji dadin ganin gwamnan CBN ya kaucewa gurfana a gaban shari’a ba.
Emefiele wanda ya yi yunkurin samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Tinubu ya zargi Gwamnan na CBN da bullo da tsarin sake fasalin kudin Naira da kuma kirkirar rashin tsabar kudi a hannun Jam’ar kasad domin yi masa zagon kasa.
A wani labarin kuma, FG Na Kashe Miliyan N1m Duk Shekara Kan Kowane Fursuna – Ministan Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce tana kashe Naira miliyan 1 duk shekara domin kula da kowane daya daga cikin fursunonin da ke gidajen gyaran hali a kasar nan,Punch ta rawaito.
Sola Fasure, mai baiwa ministan harkokin cikin gida shawara kan harkokin yada labarai, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Asabar a Abuja.