Kwamitin Rikon kwarya da kula tsare-tsaren gudunarwa na jam’iyyar APC (CECPC) na Kasa baki daya, ya nesanta kansa da Shugabancin bangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam’iyyar a jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar na kasa, wanda ya bayyana matsayinsa kan taron da aka ce jam’iyar ta gudanar ya ce, ba a aike da kwamatin jam’iyar zuwa jihar Kano ba.
Sakataren kwamitin jam’iyar APC na Kasa CECPC, John Akpanudoedehe, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya ce, jam’iyyar ba ta mallaki kwafin hukuncin wata babbar kotun Abuja da aka ce ta amince da bangaren Shekarau ba.
Jaridar PlatinumPost ta rawaito cewa an yi takun saka tsakanin bangaren Shekarau na APC da bangaren zartaswar jam’iyyar APC na jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta, Abdullahi Abbas.
Shugaban jam’iyyar APC da aka sani yana biyayya ne ga Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Da yake magana game da hukuncin kotun, Akpanudoedehe ya ce : “Mu ne shugabannin jam’iyyar kuma ba za mu so yin tsokaci kan hukuncin da ba mu gani ba a gaban mu.
”Abin da zan iya gaya muku yanzu shi ne, za mu nemi takardar shedar ta gaskiya. Ba mu gani ba a halin yanzu. Muna bukatar mu yi nazari akan hukuncin.”
Da aka nemi jin ta bakinsa dangane da rade-radin da ake yi cewa jam’iyyar APC ta aika wasu kwamitoci guda biyu jihar Kano, domin gudanar da zaben Shuwagabannin jihar, Akpanudoedehe ya yi watsi da hakan, inda ya bayyana zancen a matsayin zargin da ba shi da tushe balantana makama.
“Ba mu ba wa kwamitoci biyu wasiku ba. Ta yaya za mu yi hakan? Ba za mu kunna wuta a gidanmu ba, mun san mutanen da muka ba wasiƙar su je Kano su gudanar da aikin zaben a hukumance.”
A wata hira ta daban, Barista Auwwal Ibrahim wanda ya jagoranci tawagar da ta gudanar da taron zaben a jihar, wadda ta samar da Abdullahi Abass a matsayin shugaba, ya shaida wa manema labarai cewa taron da Gwamna Ganduje ya halarta ita ce ta gaskiya.
Ya kara da cewa tawagarsa ta mutum bakwai kowannensu ya samu takarda a hukumance daga jam’iyyar APC na kasa.
Ya ce: “lamarin anyi adalci saboda an zabo mu ne, daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa da sunana da sunayen mambobinmu. Mun karbi aikin mu ne daga hedikwatar jam’iyyar APC ta ofishin Farfesa Al Mustapha Mednaer.”
“Mun je taron ne da dukkan kayan aiki kuma mun gudanar da taron a Kano ba tare da wata tangarda ba. Mun gana da duk masu ruwa da tsaki tun daga kan Gwamna har zuwa kwamitin shirya taron na cikin gida. Mun yi abin da muka yi muka dawo da sakamakon sakatariyar jam’iyar APC na kasa.” Inji shi.
“Dukkan membobina suna tare da ni. Ina da Hotunan, da ke nuna cewa muna tare a Taron zaben daya gudana. Mu bakwai ne gaba daya kuma kowa ya sanya hannu kan takardar sakamako da rahoton da muka tattara.”
Da aka tambaye shi ko yana da masani akan wani Taron makamancin wannan a Kano?, Barista Abdullahi ya mayar da martani.
“Ina sane da hakan a ranar taron. A yayin da ake ci gaba da gudanar da taron, shugaban kwamitin shirya taron na karamar hukumar wanda ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Kano a wani lokaci ya kira ni ya sanar da ni cewa an yi wani taron kama-da-wanda da ake yi a kusa da wani kauye, dake makwaftaka da farfajiyar gidan yari na jihar.”
“Na shaida musu cewa a halin da ake ciki an aiko ni ne daga hedkwatar kasa tare da umurtar in zo in gudanar da taron. Don haka na ce masa ni ne shugaban kwamitin gudanar da Taron zaben na gaskiya, kuma muna da yarda da yarjejeniya daga hedkwatar jam’iyar na kasa, da mu zo mu gudanar da aikin. Na gaya masa cewa ba ni da masaniyar duk wani taro mai kama da Wanda nake jagoranta, da ke gudana kuma na gaya masa cewa, jam’iyyar ba za ta amince da su ba.”