Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta kasa (IPMAN) ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da barazanar da wasu ‘yan kasuwa a shiyyar Kudu maso gabas ke yi na rufe gidajen man da ke Calabar da Fatakwal da kuma Enugu.
Mista Edet Umana, Shugaban IPMAN na Cross River ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar din nan.
Umana ya yi Allah-wadai da barazanar da aka yi na rufe gidanjen man saboda cin zarafin ‘yan sanda da wasu ‘yan kasuwar yankin suka yi.
Ya ci gaba da cewa ‘yan kungiyar IPMAN na shiyyar ba su da sha’awar haifar da cikas a harkar samar da man fetur sakamakon kalubalen da aka fuskanta kwanan nan a fadin kasar nan.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/kungiyar-kwadago-nlc-ta-nemi-buhari-ya-kara-albashi-da-kashi-50/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Umana ya ce: “An warware matsalar shugabancin kungiyar ta IPMAN ne bisa hukuncin da kotun koli ta yanke a Abuja ranar 14 ga Disamba, na shekarar 2018.
“Hukuncin da mai shari’a Musa Muhammad ya karanta a kara mai lamba SC15/2015 ya amince da Mista Chinedu Okoronkwo da Alhaji Danladi Pasali a matsayin shugabannin kungiyar IPMAN ta kasa.
A cewarsa, a kan wannan hukunci, rundunar ‘yan sandan ta gayyaci wasu mutanen yankin Kudu maso gabas da ke ikirarin cewa su ne bangaren IPMAN domin yin taro kan lamarin.
Umana ya ce matakin wanda babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Mista Usman Baba ya jagoranta na da nufin nemo mafita mai dorewa a rikicin shugabancin.
Ya ce rashin yin biyayya ga hukuncin kotun ne ya sa ‘yan sandan shiga tsakani bisa shawarar babban lauyan gwamnatin tarayya, Mista Abubakar Malami.
Umana ya bukaci ‘yan kungiyar IPMAN da su rika gudanar da sana’o’insu ba tare da wata fargaba ba.
Ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga kokarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da samar da man fetur da kuma rarraba man fetur din a fadin kasar nan.
(NAN)