Ba na Tsoron Ɗaukaka ƙara – Gawuna bayan hukuncin kotun Kano
Dan Takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen Gwamnan Jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, Nasir Yusuf Gawuna ya ce bai ji tsoron ɗaukaka ƙarar Abokin Hamayyar shi ya ce zai yi ba, yana kalubalantar nasarar da ya samu a kotu.
A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaɓen Gwamnan Kano ta bayyana ɗan Takarar Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen tare da tuɓe Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Tawagar Alƙalan ta bayar da umarnin a ba wa Gawuna Takardar shaidar zama sahihin Gwamnan Jihar Kano tare kuma da janye Takardar shaidar da aka ba Abba Kabir Yusuf.

Kotun ta lura da cewa, ba a buga tambari ko sanya hannu a katin zabe na kuri’u 165,663 ba, don haka ba su da inganci sannan ta cire adadin ƙuri’u 165 663 daga jimillar ƙuri’un Abba Kabir Yusuf.
KARANTA WANNAN LABARIN:Na Gwammace in yi aiki Mai Tasiri Cikin wa’adi 1 da inyi Wa’adi 2 marar Amfani – Gwamnan Eno
Da yake magana da BBC Hausa a wata hira da ta yi da shi yayin da yake tsokaci kan hukuncin kotun, Gawuna ya ce “Ina godiya ga Allah da ya ba mu nasara a zaɓen Jihar Kano da kotu ta tabbatar a yau Laraba.
Ina gode masa bisa nufinsa da ya zaɓe mu mu yi shugabanci, ina kuma gode wa lauyoyinmu da sauran jama’a bisa addu’o’i da goyon bayan da suka ba mu”.
Ya ƙara da cewa, tun farko an ayyana Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin wadda ta lashe zaɓen, amma ya yi imanin cewa Allah ya riga ya yanke hukuncin cewa suna da ‘yancin ƙalubalantar sakamakon a kotu kuma sun yi hakan.
Gawuna ya ce duk wanda ya yarda cewa babu abin da ke faruwa ba tare da yardar Allah ba, to ba zai taɓa damuwa ko daukar mulki a matsayin abin ayi ko a mutu ba, yana mai jaddada cewa duk abin da ya same su sun yi imani da nufin Allah ne.
A cewarsa “Ba ma tsoro domin mun san cewa duk abin da ya faru na alheri ne Allah ba ya kuskure.”