Wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mai suna, Darlington Onyelike, ya shawarci mata da kada su bari soshiyal midiya ta ruɗe su, su yarda cewa namiji da mace daidai da juna suke a aure.
Onyelike, wanda ya bayyana hakan a wani rubutu da yayi a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, ya kuma janyo hankalin matan aure kan cewa mazajen su ba abokan su bane, saidai iyayen gidan su ne. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Aikin Barna: Obi yayi Allah wadai da harin Kano akan Buhari
“Babu daidaito tsakanin namiji da mace a aure, ku daina ruɗar da kan ku, ba a yin sarki biyu a gida ɗaya, guda ɗaya ne kawai shine mijinki. Mijinki shine jagora a gidan.”
“Mijinki ba abokin ki bane, ubangidan ki ne. Mafi yawan waɗanda suke cewa sun auri abokan su duk auren su ya mutu. Sannan ba yadda mijinki ya mayar da hankalin shi a kanki har na tsawon sa’o’i ashirin da huɗu, shin ba zai fita yaje ya yayi aiki ya nemo muku abinda zaku ci ba?”
“Hakan na nufin zai tsaya da ke kenan tun daga safe har dare? Ba abu bane mai yiwuwa, mu daina yaudarar kan mu a soshiyal midiya. Ko mara aikin yi ba zai taɓa iya mayar da hankalin sa kan mace har na tsawon sa’o’i ashirin da huɗu ba.” A cewar sa.
Sai Kace Zan Yi Sadaka: Wani Matashi Ya Koka Bayan Banki Ya Lafkeshi Da Takardun Kuɗi Na N5
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka bayan yaje banki an lafkeshi da ƙananan kuɗaɗe.
Wani matashi ɗan Najeriga ya koka kan takardun kuɗin da aka bashi lokacin da yaje ciro kuɗi a banki.
A cewar matashin, tarin ƴan naira biyar (N5) kawai aka lafke shi da su lokacin da yaje wani reshen bankin sa domin ciro kuɗi.