Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Juma’a, ya ce kuskure ne a bangaren masu laifi da masu fashi da makami su dauka cewa suna yaki ne don addini.
Shehu Sani, wanda ya rubuta a shafin sa na Facebook da aka tabbatar, ya ce ba za a taba daukar su a matsayin masu yaki mai tsarki ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ga Google: Ku Hana Kungiyar IPOB Shiga Dandalin Ku
Sanata Shehu Sani ya rubuta cewa: “Sun yi ikirarin cewa suna yaki ne don addini. Sun kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Suna yin garkuwa da su har da mata da yara na tsawon watanni ko shekaru. Wani lokaci su kan yi fyade tare da cin zarafin wadanda abin ya shafa.”
A cewarsa, suna jawo wa iyalai wahala da kunci tare da karbar kudin fansa.
“Wannan kuma ba zai taba zama yaki don addini ba. Kuma ba za su taɓa zama mayaka masu tsarki ko wadanne iri ba. Suna rayuwa ne kawai da takobi… ”in ji shi.
A wani Labarin Kuma Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hula, Coalition for Good Governance (COG) sun amince da dan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a zaɓen 2023.
Gamayyar dai ta kunshi jam’iyyun siyasa 15 da aka soke rajista a kasar da kuma wasu tsoffin ƴan takarar shugaban kasa.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa Hannun Shugaban su na Ƙasa Engr. Okey Chikwendu da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Don Anthony Harmattan, Ƙungiyar sun bayyana Obi da abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin wanda ya fi kowa amincewa a tsakanin sauran ‘yan takara.
“Zabin ya ta’allaka ne kan tantance tikitin tare da ’yan takara masu sahihanci wadanda aka gwada, amana da kuma nuna isashen basira don ceto al’ummarmu daga halin da muka tsinci kanmu a ciki da kuma biyan bukatun al’ummar Nijeriya wanda yake daidai da adalci ba tare da la’akari da ƙabila ko ɓangaren ci.
“Saboda haka mun amince da sake canza ma ofisoshinmu suna a fadin kasar a matsayin ofisoshin yaƙin neman zaɓe. Tsarin mu a duk fadin Jihohi 36 da kananan hukumomi 774 za su goyi bayan tikitin Peter Obi/ Datti Baba-Ahmed karkashin jam’iyyar Labour,” in ji sanarwar.