Ba za ka bar APC ba – Shettima ga Tsohon Gwamna Bindow
Mataimakin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya kai wa tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Jibrilla Bindow ziyara.
Bindow wanda ya kasance Gwamnan Jihar Adamawa a tsakanin Shekarar 2015 zuwa 2019, ya sha kaye a zaben 2019 saboda rikicin da ya barke tsakanin wasu jiga-jigan jam’iyyar, akalla biyu daga cikin wadanda aka ce sun hana shi samun kuri’u.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane, Masu Damfara Ta Yanar Gizo, Da Sauran Masu Laifi
Ya nemi Tikitin Takarar Gwamna na jam’iyyar a Zaɓen 2023 amma rahotanni sun nuna cewa ya sha kaye saboda ƴan takarar biyu da suka fi shi kuri’u sun yi amfani da hanyoyin da bai bi ba.
Don haka ne aka riƙa raɗe-raɗin cewa zai fice daga jam’iyyar APC, amma Shettima tare da rakiyar wasu fitattun ƴaƴan jam’iyyar APC, sun je gidan Bindow da ke Abuja ranar Alhamis inda suka nemi ya ci gaba da zama mamba a jam’iyyar APC da goyon bayan Jam’iyyar a Zaɓen 2023 mai zuwa.
A cewar wata kafar yada labarai ta Adamawa karkashin wani tsohon mai taimaka wa Bindow, Shetima ya bukaci tsohon gwamnan Adamawa da kada ya sanya ido a kan shirin ficewa daga jam’iyyar saboda ya yi aiki da yawa.
Shettima ya ce yana sane da cewa Bindow ya sha wahala sosai saboda rikicin cikin gida na jam’iyyar amma ana ƙoƙarin haɗa kan ƴaƴan Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa.
“Dan’uwana, ka yi aiki da yawa don Jam’iyyar nan, ba zan iya kallon ka ka bar mu ba. Muna tare a kan manufar lashe zaben 2023,” Shettima ya shaidawa Bindow.