Kungiyar kare muradan al’ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta ja hankalin gwamnatin Nijeriya a kan ta hanzarta ɗaukar mataki game da yadda ake samun wasu matasa da almajirai suna kwarara zuwa yankunan kudu daga arewacin Nijeriya ba.
BBC sun labarto cewa; a baya-bayan nan dai ana ta yada bidiyon yadda ake kama matasa cikin tireloli a wasu jihohin kudancin Nijeriya, da ake cewa sun fito ne daga arewa, ko da yake babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro da ta tabbatar da hakan.
Wannan na faruwa ne duk da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi da gwamnatin Nijeriya da ma na wasu jihohin suka kafa da nufin hana yaduwar cutar korona.
Sai dai kungiyar ta ce ta gano cewa mutanen na ketawa ne ta dazuka domin shiga yankunan.
Dr John Nwodo, shi ne shugaban kungiyar na Naieriya, ya ce akwai damuwa game da yadda hukumomi suka yi shakulacin ɓangaro kan kiraye-kirayen da suke ta yi na dakile wannan matsala.